Real madrid tacire liverpool sau uku kenan ajere daga gasar chamion ajere da sauran labarai

Football news 77
0


 Real Madrid ta doke Liverpool da cin 1-0 a wasa na biyu a

Champions League, zagayen 'yan 16 da suka kara a Santiago

Bernabeu.

Karim Benzema ne ya ci wa Real kwallon da take bukata, ta

kuma kai zagayen daf da na kusa da na karshe.

Kenan kungiyar Sifaniya ta fitar da ta Ingila da cin 6-2 a karawa

gida da waje a bana.

Ranar 21 ga watan Fabrairu, Real ta ci Liverpool 5-2 a wasan

farko a Anfield a gasar zakarun Turai ta bana.

A bara Real ta doke Liverpool 1-0 a Faransa ta dauki

Champions League na 14 jimilla, karo na biyu da ta dauki kofin

a kan Liverpool a tarihi.

A kakar 2017/18, Real ta ci Liverpool 3-1 a Lisbon ta lashe

Champions League.

Sun yi wasa 11 a tsakaninsu, Real ta ci bakwai, Liverpool ta yi

nasara a uku da canjaras daya.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar

maki tara tsakaninta da Barcelona ta biyu a bana, ita take rike

da Champions League.

Ranar 19 ga watan Maris, Real za ta ziyarci Barcelona a gasar

La Liga da za su buga a Camp Nou, karawar hamayya ta El

Clasico.

Ita kuwa Liverpool tana ta shida a Premier League da maki 42,

bayan da Arsenal ke jan ragama mai maki 66, bayan wasan

mako na 27.

Sai a ranar 1 ga watan Afirilu Liverpool za ta ziyarci

Manchester City, domin buga wasan Premier League a Etihad.

Tun farko an dage karawar da Liverpool ya kamata ta buga da

Fulham ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)