Sporting ta fitar da Arsenal a Europa League dama sauran labarai

Football news 77
0


Arsenal ta yi ban kwana da Europa League na bana, bayan da

Sporting ta fitar da ita a bugun fenariri a Emirates ranar

Alhamis.

Tun farko sun tashi 1-1, inda Granit Xhaka ya ci kwallon a

minti na 19, kuma na biyar da ya zura a raga a kakar nan a

dukkan fafatawar da ya yi wa Arsenal.

Sporting ta farke ta hannun Pedro Goncalves, bayan da suka

koma zagaye na biyu a fafatawar.

Gabriel Martinelli ya buga ta sa fenaritin amma golan Sporting,

Adan ya tare kwallon da haka kungiyar Portugal ta kai zagayen

baga da cin 5-3.

Sporting ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da

aka bai wa Pedro Goncalves jan kati.

A makon jiya Gunners ta tashi 2-2 a gidan Sporting a wasan

zagayen farko na kungiyoyi 16.

 


Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)