BREAKING NEWS: Masu garkuwa da mahaifin Diaz sun bukaci a ba su tsaro

Football news 77
0
Yan tawayen da suka yi garkuwa da mahaifin Luis Diaz, sun bukaci a ba su tsaro, kafin su sako shi. 'Yan tawayen da ake kira 'The National Liberation Army' ko 'ELN' a takaice sun ce neman inda suka ajiye mahaifin dan kwallon Liverpool da sojoji da 'yan sanda ke yi zai iya kawo tsaikon sako shi, kamar yadda jaridun Colombia suka waw llafa. An kama Luis Manuel Diaz tare da matarsa a Barrancas cikin kasar Colombia ranar 28 ga watan Oktoba ne. Dan kwallon Liverpool, Diaz ya bukaci wadanda ke rike da mahaifinsa, su sako masa shi, domin ya huta ko ya samu kwanciyar hankali. An tsinci mahaifiyar Diaz a cikin mota, bayan 'yan sanda sun kusan cimma masu garkuwan, wadanda suka tsere da mahaifin Diaz. Diaz dan wasan Colombia, ya shiga wasan da Liverpool ta ziyarci Luton Town a gasar Premier League ranar Lahadi, kuma shi ne ma ya farke kwallon da suka tashi 1-1. Ita dai ELN ta tabbatar da aniyarta ta son sakin mahaifin Diaz, nan ba da jimawa ba.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)