Arsenal na iya doke ƙungiyoyin Premier a zawarcin Declan Rice

Football news 77
0

 

Dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, shi ne

na farko da Arsenal ke son saye a bazarar nan,

kuma akwai alamun cewa Gunners ɗin za su iya doke

Chelsea da Manchester City da Manchester United

wajen sayen ɗan wasan na Ingila. (Evening Standard)

Haka ita ma Manchester United tana sa ido kan ɗan

gaban Eintracht Frankfurt Randal Kolo Muani na

Faransa tare da matashin ɗan gaban Atalanta

Rasmus Hojlund daga Denmark ko da burin United na

sayen Harry Kane, bai tabbata ba. (Manchester

Evening News)

Ita kuwa Real Madrid ta karkata ne kan matashin

ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund Jude

Bellingham, a matsayin wanda ta fi son ganin ta

saya, bayan shi kuma kulob ɗin na son sayen ɗan

bayan Chelsea Reece James daga Ingila. (AS)

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)