Benzema ya yaga barakar Barcelona a Copa del Rey

Football news 77
0

 

Real Madrid ta kai wasan karshe a Copa del Rey, bayan da ta
doke Barcelona 4-0 a wasa na biyu ranar Laraba a Nou Camp.




Daf da za su je hutu Vinicius Junior ya ci wa Real kwallon
farko, Karim Benzema ya kara na biyu minti biyar da komawa
zagaye na biyu.


Tsohon dan wasan tawagar Faransa shine ya ci na uku, kuma
na biyu a wasan hamayya na El Clasico a bugun fenariti.
Daf da za a tashi kenan Benzema ya kara na uku na hudu 




karo na biyu a jere yana cin uku rigis a Real Madrid.
A karshen mako Real ta caskara Valladolid 6-0, inda Benzema
ya ci uku rigis a karon farko a bana a Real Madrid.
Real Madrid ta kai zagayen gaba da cin kwallo 4-1 gida da
waje, bayan da Barcelona ta yi nasarar cin 1-0 a wasan farko
ranar 2 ga watan Maris.
Wasa na biyar kenan da aka kara tsakanin manyan kungiyoyin
Sifaniya, Barcalena ta yi nasara a uku, Real Madrid ta ci biyu.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)