Tuchel bai yi bacci ba kan zai fuskanci Guardiola

Football news 77
0


 Kociyan Bayern Munich, Thomas Tuchel ya ce ya kasa bacci

sosai, saboda zai kara da Pep Guradiola na Manchester City

ranar Talata a Eihad.



City za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan farko a

Champions League, zagayen quarter finals.

Karon farko da Tuchel zai ziyarci Ingila tun bayan da Chelsea ta

kore shi a watan Satumba ta maye gurbinsa da Graham Potter.

A karawa 10 tsakanin kociyoyin biyu da suka yi, wasa uku

Tuchel ya yi nasara a kan Pep Guardiola.



''Idan kana son yin shiri mai kyau ka kwanta da wuri ka samu

hutu, sai dai na kasa bacci yadda ya kamata da na kwanta.''

Karawar karshe da Tuchel ya ci Guardiola ita ce a 2021 lokacin

da Chelsea ta doke City ta lashe Champions League, kuma na

farko daga cikin uku da ya lashe a kungiyar a wata 20 a

Stanford Bridge.



Daga baya Pep Guradiola ya doke Chelsea karo biyu a Premier

League, san nan aka kori Tuchel daga Stamford Bridge.

Rabon da City ta fuskanci Bayern tun Nuwambar 2014

karkashin Manuel Pellegrini, inda kungiyar Etihad ta yi nasara

3-2 ta kai zagayen 'yan 16 a Champions League.

Tuchel, wanda ya maye gurbin Julian Nagelsmann ya ce dole

sai sun saka kwazo idan suna son yin galaba a kan City,

wadda ta yi nasara a karawa takwas a dukkan fafatawa.

Wasan na ranar Talata zai bai wa mai tsaron bayan Bayern

Munich, Joao Cancelo fuskantar kungiyarsa City, wadda ta

bayar da aronsa a watan Janairu.



Mai shekara 28 baya samun buga wasa sosai a City, dalilin da

ya sa ya bukaci motsawa, wanda ya koma Bayern da cewar za

ta iya sayen shi fam miliyan 61.4 a karshen kakar nan idan ya

taka rawar gani.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)