Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki 12 a La Liga

Football news 77
0

 


Barcelona ta ci Real Madrid 2-1 a wasan mako na 26 a gasar

La Liga da suka kara a Camp Nou ranar Lahadi.

Real ce ta fara cin kwallo a minti na tara da fara wasa, bayan

da dan kwallon Barcelona, Ronald Araujo ya ci gida.

Daf da za su je hutu Barcelona ta farke ta hannun Sergi

Roberto, an kuma kusan tashi daga fafatawar ta kara na biyu ta

hannun Franck Kessie

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta daya

a kan teburin La Liga da maki 68, Real Madrid ce ta biyu mai

56, kenan da tazarar maki 12 tsakani.

Wannan shine karo na hudu da suka fuskanci juna daga biyar

da za su buga a tsakaninsu a wasannin Sifaniya a bana.

Real Madrid ta fara cin Barcelona 3-1 a gasar La Liga cikin

Oktoban 2022 a La Liga a Santiago Bernabeu.,

Sai dai Barcelona ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia a

cikin watan Janairu da cin 3-1 a kan Real Madrid.

Haka kuma Barcelona ta ci Real Madrid 1-0 a wasan farko na

daf da karshe a Copa del Rey da suka buga a Santiago

Bernabeu a farkon makon watan Maris.

Ranar 5 ga watan Afirilu, Barcelona za ta kara karbar bakuncin

Real Madrid a wasa na biyu na daf da karshe a Copa del Rey a

Nou Camp.

Real Madrid wadda ta lashe UUefa Super Cup da Fifa World

Club Cup a bana ta kai daf da na kusa da na karshe a

Champions League.

Wadda ita ke rike da kofin bara na 14 jimilla za ta kece raini da

Chelsea gida da waje a cikin watan Afirilu.

Barcelona za ta je gidan Elche a wasan mako na 27 a La Liga

ranar 1 ga watan Afirilu.

Ita kuwa Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Valladolid ne

ranar 2 ga watan Afirilu a fafatawar mako na 27 a La Liga a

Santiago Bernabeu.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)