Ibrahimovich ya doke tarihin da Dino Zoff ya kafa shekara 20

Football news 77
0

 

Sweden ta sha kashi da ci 3-0 a gida a hannun Belgium ranar

Juma'a a wasan farko a rukuni na shida a neman shiga Euro

2024 da za a buga a Jamus.

Romelu Lukaku ne ya ci wa Belgium kwallo uku rigis a wasan

farko da Kevin de Bruyne ya fara aikin kyaftin din tawagar,

bayan maye gurbin Eden Hazard.

Bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar da Belgium ba ta

taka rawar gani ba, Hazard ya sanar da yin ritaya, ya mayar da

hankali a Real Madrid.

Zlatan Ibrahimovich ya buga wasan ya kuma karya tarihin da

Dino Zoff ya kafa kusan shekara 20 a matakin mai shekaru da

yawa da ya buga wasannin.

Zoff ya kafa bajintar ranar 29 ga watan Mayun 1983 a karawar

Sweden da Italiya, wanda ya buga wasan yana da shekara 41

da kwana 90.

Ibrahimovich ya yi karawar ta ranar Juma'a yana da shekara 41

da kwana 172, yayin da tsohon golan Italiya ya yi wasan yana

kusan cika shekara 40 da haihuwa.

Sweden ta gayyaci Ibrahimovich, domin buga mata tamaula,

bayan shekara daya rabon da ya taka mata leda.

Ya yi ritaya da buga wa Sweden tamaula bayan Euro 2016 daga

baya ya koma taka leda a 2021, inda kasar ta kasa samun

tikitin shiga kofin duniya a Qatar a 2022.

Ibrahimovic, ya buga wa AC Milan wasa uku a bana, fafatawa

ta karshe da ya yi wa Sweden ita ce da Poland da suka yi

rashin nasara a neman zuwa Qatar.

Tsohon dan kwallon Manchester United da Paris St-Germain,

shine kan gaba a ci wa Sweden kwallaye a tarihi mai 62 a

wasa 121.

To sai dai kuma ranar Juma'a Girka ta je ta doke Gibralta 3-0

a wasan farko a rukuni na biyu a neman shiga Euro 2024.

Lee Casciaro ya buga wa Gibralta wasan yana da shekara 41

da kwana 176, kenan shi da Ibrahimovich suka kafa tarihin

masu yawan shekarun haihuwa da suka buga wasan a tarihi

kenan.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)