Tottenham na zawarcin Henderson, Wilfried ya ja hankalin kungiyoyi

Football news 77
0


 Manchester United na iya amfani da kwadayin da Tottenham

ke nunawa kan mai horar da raga Dean Henderson, wajen

ganin su matsa mata ta sayar musu da dan wasan Ingila, Harry

Kane. (ESPN)

Dan wasan Eintracht Frankfurt mai kuma bugawa Faransa gaba

Randal Kolo Muani, wanda Manchester United ke harinsa kan

fam miliyan 150, ya nuna cewa a shirye yake ya bar kungiyar.

(L'Equipe, via Mail)

Manchester City ta sake dawo da batun kwadayinta kan dan

wasan Bayer Leverkusen mai shekara 19 Florian Wirtz. (90min)

Tottenham na iya rasa damarta na dawo da tsohon kocinsu

Mauricio Pochettino, saboda zawarcin da Real Madrid ta soma

nunawa, musamman idan Carlo Ancelotti ya tafi.(Times)

Chelsea ta yarda da cewa zata yi asara idan ta sayar da dan

wasanta Romelu Lukaku, a karshen kaka. (Football Insider)

Arsenal, Chelsea da Manchester City sun nuna kwadayinsu kan

dan wasan Italiya Wilfried Gnonto daga Leeds United.

(Gazzetta dello Sport, via Metro)

Juventus da Napoli na cikin kungiyoyin Italiya da ke son su ma

su saye Gnonto. (90min)

Arsenal da Barcelona na fatan saye dan wasan Sifaniya Martin

Zubimendi daga Real Sociedad. (Mail)

Barcelona na son sayo dan wasan Monaco mai shekera 21

Vanderson. (Sport - in Spanish)

Kungiyoyi da dama na nuna zawarcinsu kan dan wasan Ingila

Brandon Williams, mai shekara 22, daga Manchester United.

(Football Insider)

Dan wasan Juventus Adrien Rabiot, na iya tafiya Liverpool.

(Sun)

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)