'Yan wasan Najeriya da za su kara da Guinea gida da waje

Football news 77
0



 Tawagar kwallon kafa ta Najeriya za ta kara da ta Guinea

Bissau a wasan neman shiga gasar kofin Afirka a Abuja ranar

Juma'a.

Tun ranar 19 ga watan Maris 'yan wasan da Super Eagles ta

gayyata suka isa sansanin tawagar, domin atisayen tunkarar

karawar gida da waje.

Cikin wadanda Jose Santos Peseiro ya gayyata har da kyaftin

Ahmed Musa da Victor Osimhen da Ademola Lukman da karin

wasu 20.

Najeriya za ta fara kece raini ranar Juma'a a filin wasa na

Moshood Abiola a Abuja da yammaci, sannan su buga wasa

na biyu ranar 27 ga watan Maris a Bissau.

Super Eagles ce ta daya a rukunin farko da maki shida, bayan

da ta doke Saliyo da Sao Tome, ita kuwa Bissau tana ta biyu

da maki hudu, bayan doke Sao Tome da canjaras da Saliyo.

Alkalin wasa shine Mahmoud Elbana, wanda zai yi aiki tare da

Youssef Elbosaty da Sami Halhal da kuma Ahmed El-

Ghandour, dukkansu daga Masar.

Kwamishinan karawar shine Prosper Harrison Addo daga

Ghana, yayin Kotey Alexander zai auna kwazon alkalan wasan

ranar Juma'a.

Jerin 'yan wasan Super Eagles:

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Victor

Sochima (Rivers United); Kingsley Aniagboso (Giant Brillars)

Masu tsaron baya: Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich

Albion, England); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce SK,

Turkey); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany);

Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Calvin Bassey (FC Ajax,

The Netherlands); Daniel Bameyi (YumYum FC); Zaidu Sanusi

(FC Porto, Portugal); Bruno Onyemaechi (Boavista FC,

Portugal)

Masu buga tsakiya: Wilfred Ndidi (Leicester City, England);

Frank Onyeka (Brentford FC, England); Alex Iwobi (Everton FC,

England); Joe Aribo (Southampton, England)

Masu cin kwallaye: Kelechi Iheanacho (Leicester City,

England); Ahmed Musa (Sivasspor K, Turkey); Samuel

Chukwueze (Villarreal CF, Spain); Moses Simon (FC Nantes,

France); Ademola Lookman (Atalanta BC, Italy); Terem Moffi

(OGC Nice, France); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Paul

Onuachu (Southampton FC, England)

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)