Yan Real 13 aka gayyata don yi wa tawagoginsu wasa

Football news 77
0

 


'Yan wasan Real Madrid 13 aka gayyata tawagoginsu, domin

buga wa kasashensu tamaula a makon nan da na gobe.

A cikin makon nan za a buga wasannin neman gurbin shiga

gasar nahiyar Turai da na Afirka da kuma wasannin sada

zumunta.

Wadanda aka gayyata sun hada da Carvajal da Nacho da

kuma Ceballos daga Sifaniya, Courtois daga Belgium,

Camavinga da Tchouameni daga Faransa.

Wasannin da za a buga a makon nan da na gobe

Kociyan tawagar Sifaniya ya gayyaci Carvajal da Nacho da

kuma Ceballos, domin buga fafatawar neman shiga Euro 2024.

Courtois zai buga wa Belgium wasan shiga European

Championship rukuni na shida ranar Juma' a da Sweden kwana

hudu tsakani da Jamus a wasan sada zumunta.

Camavinga da Tchouameni za su buga wa Faransa wasannin

shiga UEFA EURO 2024 da za ta kara da Netherlands a Faransa

da kuma Ireland a Dublin Arena.

Luka Modrić zai yi wa Croatia wasannin neman gurbin shiga

European Championship a fafatawa da Wales ta ziyarci Turkey.

David Alaba yana cikin 'yan wasan Austria da za su buga mata

wasa biyu a neman gurbin shiga Euro 2024 da za ta fafata da

Azerbaijan da kuma Estonia.

Tawagar Ukraine ta gayyaci Lunin , domin ya buga mata wasan

da za ta yi da Ingila a neman gurbin Euro 2024.

Brazil ta gayyaci Vini Jr da Militão da kuma Rodrygo, domin su

yi mata wasan sada zumunta da Morocco ranar Asabar.

Valverde zai buga wa Uruguay wasan sada zumunta da za ta

buga da Japan da kuma South Korea.

Real Madrid Kwallon kafa Wasanni

Me ya sa za ku iya aminta da BBC

Sharuddan yin amfani

A game da BBC

Ka'idojin tsare sirri

Ka'idoji

Tuntubi BBC

AdChoices / Do Not Sell My

Info

© 2023 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu

shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi

dangane da adireshin waje.

GETTY IMAGES

Spain da Norway ranar Asabar 25 ga watan Maris

Scotland da Spain Talata 28 ga watan Maris

Sweden da Belgium Juma'a 24 ga watan Maris

Jamus da Belgium Talata 28 ga watan Maris

Faransa da Netherlands Juma'a 24 ga watan Maris

Ireland da Faransa ranar Litinin 27 ga watan Maris

Croatia da Wales Asabar 25 ga watan Maris

Turkey da Croatia Talata 28 ga watan Maris

Austria da Azerbaijan Juma'a 24 ga wayan Maris

Austria da Estonia ranar Litinin 27 ga watan Maris

Ukraine da Ingila Lahadi 26 ga watan Maris

Morocco da Brazil Asabar 25 ga watan Maris

Japan da Uruguay Juma'a 24 ga watan Maris

South Korea da Uruguay Talata 28 ga watan Maris

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)