Real Betis ta ziyarci Manchester United, domin buga wasan
farko a zagayen 'yan 16 a Europa league na bana.
United ta kawo wannan matakin bayan da ta yi waje da
Barcelona a karawar da suka yi gida da waje a fafatawar cike
gurbi.
Ita kuwa Betis ita ce ta yi ta daya a rukuni na uku da maki 16,
Roma ta yi mata ta biyu da maki 10.
United za ta buga wasan ba tare da Marcel Sabitzer da kuma
Anthony Martial, wadanda ke jinya.
Har yanzu Christian Eriksen da Donny van de Beek, sun dade
suna jinya.
Real Betis ta rasa dan wasan gaba mai cin kwallaye, Nabil
Fekir, wand ke jinya har zuwa karshen kakar bana.
Wannan shine karon farko da United da Betis za su fuskanci
juna a tsakaninsu.
A wasa biyar baya a gasar zakarun Turai da United ta buga da
kungiyoyin Sifaniya ta yi rashin nasara - ta yi rashin nasara a
hannun Real Sociedad a Satumba a fafatawar cikin rukuni.
Ranar Lahadi, Liverpool ta ci United 7-0 a wasan Premier
League a Anfield, ita kuwa Betis ta tashi 0-0 da Real Madrid a
karshen mako a La Liga.
United na fatan daukar kofi hudu a bana, bayan da ta dauki
Carabao Cup tana zagayen quarter final, za ta kara da Fulham
nan gaba.
Tana buga Europa tana kuma ta uku a kan teburin Premier
League.
Manchester United ta taba lashe Europa League a kakar
2016/17 karkashin Jose MourinReal Betis ta ziyarci Manchester United, domin buga wasan

2016/17 karkashin Jose Mourinho, ita kuwa Betis na fata.ho, ita kuwa Betis na fata.