Lewandowski da Gavi za su buga wasa da Athletic Bilbao

Football news 77
0


Athletic Bilbao za ta karbi bakuncin Barcelona a gasar La Liga
mako na 25 da za su fafata ranar Lahadi.
Ranar 23 ga watan Oktoban 2022, Barcelona ta doke Athletic
4-0 a Camp Nou, Ousmane Dembele da Sergi Roberto da
Robert Lewandowski da kuma Ferran Torres suka ci mata
kwallayen.
Barcelona tana mataki na daya a kan teburi da maki 62, ita
kuwa Athletic tana ta tara mai maki 33.
Barca wadda keda tazarar maki shida tsakaninta da Real
Madrid na fatan ya koma tara idan ta yi nasara a gidan Athlelic
ranar Lahadi.
Ranar Asabar Real Madrid ta doke Espanyol 3-1 a babbar
gasar tamaula ta Sifaniya.
Wasan nan ba zai yi Xavi sauki ba, domin karawa daya Barca
ta yi nasara daga fafatawa shida a filin wasa na San Mames a
dukkan fafatawa.
Haka kuma tsohon kociyan Barcelona, Ernesto Valverde ne ke
jan ragamar Athletic, wanda ya dauki La Liga biyu da Copa del
Rey a Camp Nou.
Sai dai labari mai dadi shine Robert Lewandowski da Gavi
suna cikin 'yan wasan da Barcelona ta je da su Athletic, bayan
jinya da suka yi.
Amma mai tsaron baya Ronald Araujo ba zai yi fafatawar ba,
wanda aka bai wa jan kati a karawa da Valencia.
'Yan wasan Barcelona da suka je Athletic:
Ter Stegen, Sergio, Gavi, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Iñaki
Peña, Christensen, Marcos A., Jordi Alba da Kessie.
Sauran sun hada da S. Roberto, F. De Jong, Raphinha, Kounde,
Eric, Balde, Pablo Torre, Arnau Tenas da kuma A. Alarcón.
Athletic za ta yi wasan ba tare da fitatcen dan wasanta mai cin
kwallo ba, Oihan Sancet, wanda aka yi wa jan kati a karawar
da suka tashi 0-0 da Rayo Vallecano a makon jiya.
Haka kuma tana duba koshin lafiyar golanta, Unai Simón da
dan wasa Ander Herrera.


Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)