PSG, Chelsea da United na rububin Osimhen, Lukaku ya fi son yin zamansa a Inter Milan

Football news 77
0



 Manchester United na shirin dauko Joao Palhinha, dan wasan

tsakiya mai shekara 27 daga Fulham a kakar wasa mai zuwa,

sai dai kungiyoyi kamar Arsenal da Chelsea da Liverpool da

Newcastle da kuma Tottenham na sa ido kan dan kasar

Portugal din. (Sun)

Ana ganin Liverpool ce ta fi nuna sha'awar sayen Palhinha

daga Fulham. (Mail)

Dan wasan Belgium Romelu Lukaku na son yin zamansa a

Inter Milan bayan da wa'adin zamansa na aro ya kawo karshe,

sai dai kungiyar ta Italiya ba za ta iya ci gaba da biyan

albashinsa ba ga shi kuma kocin Chelsea Graham Potter bai

saka shi cikin 'yan wasan da yake son yin aiki da su ba. (Mail)

Paris St-Germain ta bi sahun Chelsea da Manchester United

wajen farautar Victor Osimhen, dan asalin Najeriya kuma dan

wasan gaba na Napoli mai shekara 24. (Nicolo Schira)

Inter Milan za ta sake kokarin sayen Victor Lindelof daga

Manchester United a karshen wannan kakar wasan bayan da ta

gaza cimma yarjejeniya da United kan dan kasar Sweden din

mai buga wasa a baya, kuma mai shekara 28 a watan Janairun

da ya gabata. (Sun)

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)