Shin sau nawa aka kara tsakanin Real da Chelsea ne? Kalli kaga👉👉👉

Football news 77
0




 


Ranar Juma'a aka raba jadawalin Champions League karawar

quarter finals, inda aka hada wasa tsakanin Real Madrid da

Chelsea.

Real ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Liverpool

da cin 6-2 gida da waje a kakar bana.

Ita kuwa Chelsea ta yi nasarar yin waje da Borussia Dortmund

da cin 2-1 gida da waje.

Sau hudu suka kara a Champions League, amma sau bakwai

suka hadu a gasar zakarun Turai jimilla.

Kungiyar da Graham Potter ke jan ragama, wadda ta kai daf da

na kusa da na karshe bayan cin Dortmund ta kuma kara da

Inter Milan da Dynamo Zagreb a cikin rukuni.

Raheem Sterling ya ci wa Chelsea kwallo uku a Champions

League a bana.

Real Madrid wadda ta ja ragamar rukuni na shida da maki 13

ta fafata da RB Leipzig da Shakhtar Donetsk da kuma Celtic

Glasgow.

Vinicius Junior na Real Madrid ya zura kwallo shida a raga a

Champions League na bana, shine kan gaba a kungiyar a kakar

nan.

Real Madrid ce za ta fara karbar bakuncin Chelsea a Santiago

Bernabeu a wasan farko ranar 11 ga watan Afirilu.

Sannan Chelsea ta karbi bakuncin wasa na biyu a Stamford

Bridge ranar 19 ga watan Afirilu.

Chelsea tana da Champions League biyu, ita kuwa Real ita ce

mai rike da na bara kuma na 14 jimilla.

Wasa tsakanin Real Madrid da Chelsea

2021/2022 Champions League

2020/2021 Champions League

1998/1999 European Super Cup

1970/1971 Euro Cup Winners Cup

Real Madrid Chelsea Kwallon kafa

Wasanni

Me ya sa za ku iya aminta da BBC

Sharuddan yin amfani

A game da BBC

Ka'idojin tsare sirri

Ka'idoji

Tuntubi BBC

AdChoices / Do Not Sell My

Info

© 2023 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu

shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi

dangane da adireshin waje.

GETTY IMAGES

Real Madrid 2 - 3 Chelsea

Chelsea 1 - 3 Real Madrid

Chelsea 2 - 0 Real Madrid

Real Madrid 1 - 1 Chelsea

Chelsea 1 - 0 Real Madrid

Chelsea 2 - 1 Real Madrid

Chelsea 1 - 1 Real Madrid

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)