Dan Aliyu ya buge Shagon 'Yar biyar, 'Yar Mage da Autan na Aisha ba kisa

Football news 77
0
Dan Aliyu na Arewa ya buge Shagon 'Yar biyar a damben gasa ranar Lahadi a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke Marabar N'yanya jihar Nasarawa, Najeriya. Bayan da Labaran dan Gwamba ya wake 'yan damben biyu ne, sai magoya baya suka ta yi musu ruwan kudi don kara musu karfin gwiwa. Nan da nan Alkalin wasa Anas Dandume ya umarci a fara damben, turmin farko ya kayatar da 'yan kallo, amma ba kisa. Bayan da suka sha ruwa suka koma turmi na biyu ne Dan Aliyu ya buge Shagon 'Yar biyar dan danben Guramada. Daga nan aka shiga daya wasan gasar tsakanin 'Yar Mage da Autan na Aisha. Turmi uku suka yi ba kisa tsakanin dan damben Kudu da na Guramada, wanda fiye da wata hudu bai fadi ba a gidan wasa da ke Marabar n'yaya .

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)