Buharin zaka yaudara. Kotu Ta Daure Wani Mutum Kan Kulla Auren Bogi Tsakanin Surukarsa Da Tsohon Shugaban Kasa Buhari - chooser5

Football news 77
0
Wata kotun majistare da ke zama a Minna, jihar Neja, ta yanke wa wani mutum mai suna Gambo Adamu hukuncin watanni 12 a gidan yari kan kulla auren bogi tsakanin surukarsa, Sa'adatu Aliyu da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Wacce ke karar, wacce ta kasance bazawara, ta tunkari kotun cewa surukinta ya karbi kudade daga hannunta wanda ya kai naira miliyan 5 bisa alkawarin hada ta aure da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust. Yadda wani mutum ya gabatarwa surukarsa sadakin aurenta da Buhari Ta fada ma kotun cewa surukinta ya gabatar mata da N100,000 a matsayin sadaki, da kwandon goro da soyayyiyar kaza a cikin wata jaka a matsayin kyauta daga Shugaban kasa Buhari a yayin daurin auren. Ta bayyana cewa bayan zaman jiran ganin tsohon shugaban kasar ya zo daukarta a matsayin sabuwar amaryarsa, sai ta yanke shawarar tunkarar kotu domin ta shiga lamarin

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)